Labarina Series: Ma'anar mai hakuri yakan dafa dutse ya sha romonsa Kallo ya koma sama, wato shaho ya suri giwa sama kamar yadda yake zarar dan tsako. Lallai Bahaushe ya yi hikima da fadin haka, domin dan tsako kadai shaho zai iya sura. Arewa24 sun saba nuna sababbin shirye-shirye da suke fito da sababbin jarumai, sai shahara da kwarewa da kayan aikin zamaninsu da kuma iya karkatar da hankalin matasa, maza da 'yan matan cikinsu.Abu na biyu wajen karkatar matasan ko a tsakankanin marubuta ita ce, shaharar marubucin wajen rubutun labari mai rike mai kallo wajen kawo rikita-rikitar da ke sakawa mai kallo son ganin ya za a karke ko ya za a warware a ko yaushe. Abin da ya ja hankalina a kan yin wannan rubutun shi ne, tun a kashi na farko wasu masharhanta suka nuna karewar labarin - wanda maudu'insa shi ne juriya da hakuri - da watakila kashi daya kawai aka nuna daga kashi 12 ko 13 ko wajejen hakan da shi ne zango daya (season one) a fim mai dogon zango (series film).
171,281 views
100,132 views
60,771 views
87,628 views
68,849 views
31,470 views
63,904 views
76,166 views
34,448 views
55,174 views
84,008 views